Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A jiya juma ‘a cewa aka gudanar da jerin gwano da gangami na ranar kudus ta duniya a fadin kasar iran dama wasu kasashen duniya daban daban domin nuna goyan baya ga alummar falasdinu da HKI take zalunta.
Makami mai linzami na Khaibar shekan da Emad 3 suna gudu da ya kai nisan kilomita 1450 da kuma 1700. Kuma yana da sauri wajen keta karfin tsaron makiya, kuma hana da karance kuskure wajen kai hari, kuma ana iya harba su takaitattun naurorin masu linzami da ma ta wayar hannun,
Idan ana iya tunawa a ranar juma’ar karshen Azumin watan Ramadan mai alfarma ne ake gudanar da gangamin ranar kudus ta duniya a nan iran dama kasashen duniya kamar yadda wanda ya asssas jamhuriyar musulunci tai ran marigayi Imam khumaini yardar Allah ta tabbata gareshi ya kafa domin nuna goyon baya ga Alummar Falasdinu da ake zalunta.
342/